Daular Islama a Yankin Khorasan (Islamic State’s Khorasan Province – ISIS-K), ƙungiyar ta’addanci ce a Afghanistan da ke gudanar da ayyuka a ƙasar da kuma Pakistan. Ƙungiyar da asali ta ƙunshi tsoffin mambobin Tehrik-e Taliban Pakistan, wato ƙungiyar Taliban ta Afghanistan, da Islamic Movement of Uzbekistan, ISIS-K ta yi mubaya’a ga ISIS a 2015. ISIS-K ce ke da alhakin kai harin Yuli na 2016 kan masu zanga-zangar lumana a Kabul da ya kashe mutum kusan 80 sannan ya jikkata wasu 230. A Agustan 2016, ƙungiyar ta ɗauki alhakin harbi da kuma harin ƙunar-baƙin-wake a wani asibiti a Quetta, Pakistan, inda aka kashe mutum 94. Kazalika, ISIS-K ta ce ita ta kai harin watan Mayun 2020 kan wani asibitin Kabul da ya kashe mutum 24, ciki har da jarirai da uwayensu.
A ranar 14 ga Janairun 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-K a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 29 ga Satumban 2015 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-K matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS-K taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da ISIS-K. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS-K kayan aiki.
