Daular Islama A Yammacin Afirka (ISIS West Africa – ISIS-WA), wani ɓangare na ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram, an ƙirƙire ta ne lokacin da ISIS-WA ta yi mubaya’a ga ISIS a watan Maris na 2015. ISIS ta karɓi mubaya’ar da ƙungiyar ta yi mata, sannan ta fara kiran kanta da suna ISIS-West Africa wato ISIS a Yammacin Afirka. Ƙungiyar da ke aiki a arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankunan Tafkin Chadi, ta kai hare-hare da dama tun daga 2016. A Nuwamban 2018, ISIS-WA ta ɗauki alhakin kai hare-hare biyar a Chadi da Najeriya da suka kashe mutum 118. A watan Mayun 2019, ISIS-WA ta ɗauki nauyin hare-hare biyu a yammacin Nijar, waɗanda suka kashe sojoji 29. A Yulin 2019, mayaƙan ISIS-WA sun kashe sojojin Najeriya 20 da na Chadi biyar yayin wani kan sansanin soja a Baga da ke Najeriyar.
Ranar 28 ga watan Fabarairun 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-WA a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 27 ga Fabarairun 2018 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-WA matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS-WA taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da ISIS-WA. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS-WA kayan aiki da gangan.
