Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga toshe hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Hamas, ko kuma Harakat al-Muqawama al-Islamiya.
Amer Kamal Sharif Alshawa, shi ne babban jagoran kamfanin gine-gine a Turkiyya na Trend GYO mai alaƙa da Hamas. Ya yi aiki a matsayin mamban majalisar zartarwa na kamfanonin zuba jarin Hamas masu yawa.
Zuwa 2018, makusantan Hamas ne ke riƙe da kusan kashi 75 cikin 100 na jarin Trend GYO. Haka nan, Hamas na da niyyar sayar da hannun jarin Trend GYO na sama da dala miliyan 15 ga manyan shugabannin kasuwancinta.
A ranar 18 ga watan Oktoba na 2023, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Alshawa a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT) bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Hakan ya sa an toshe duk wata dukiyar mutum da kuma kamfanoni da suka aikata ta’addanci, ko suke barazanar aikatawa. Ƙari kan haka, umarnin ya bai wa gwamnatin Amurka damar riƙe dukiyar mutum ko kamfanoni da ke taimakawa, ko yin aiki, ko alaƙa da ‘yan ta’adda ko ƙungiyoyin ta’addanci da aka ayyana a ƙarƙashin umarnin, har ma da rassansu, da masu shige musu gaba, da wakilansu, da abokan aikinsu.
