Ahmed Sadu Jahleb

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga toshe hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Hamas, wadda kuma ake kira da Harakat al-Muqawama al-Islamiya.

Ahmed Sadu Jahleb na cikin mambobin Hamas kuma ɗaya daga cikin masu nema mata kuɗi a Turkiyya. Jahleb na aiki ne a matsayin sakataren zuba jari na Hamas kuma yake tsara wa kamfanonin Hamas da jagororinta ayyuka.

A ranar 18 ga watan Oktoba na 2023, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Jahleb a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT) bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Hakan ya sa an toshe duk wata dukiyar mutum da kuma kamfanoni da suka aikata ta’addanci, ko suke barazanar aikatawa. Ƙari kan haka, umarnin ya bai wa gwamnatin Amurka damar riƙe dukiyar mutum ko kamfanoni da ke taimakawa, ko yin aiki, ko alaƙa da ‘yan ta’adda ko ƙungiyoyin ta’addanci da aka ayyana a ƙarƙashin umarnin, har ma da rassansu, da masu shige musu gaba, da wakilansu, da abokan aikinsu.

Skip to content