Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka 250,000 don bayanai kan Ahadon Adak, wani kwamanda a Ƙungiyar ‘Yanta Yankin Moro ta Ƙasa (Moro National Liberation Front – MNLF).
A ranar 29 ga Satumban 2009, a Tsibirin Jolo da ke Philippines, wani bam da MNLFta saka ya tashi da ayarin motocin soji. Fashewar ta kashe sojojin Amurka biyu da kuma sojan Philippines ɗaya. Waɗanda lamarin ya ritsa da su wani ɓangare ne na rundunar musamman da ke aikin jin-ƙai na gina wata makaranta. A ranar 21 ga Mayun 2010, sashen shari’a na 9th Judicial Region ya ba da umarnin kama Adak saboda alaƙa da harin.
