Abukar Ali Adan

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Adan mataimakin shugaban al-Shabaab. Ya daɗe a matsayin kwamandan al-Shabaab bayan ya jagoranci bataliyar al-Shabaab ta soja, Jabbat.

A watan Janairun 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Abukar Ali Adan a matsayin Ɗan Ta’adda na Musamman a Duniya (SDGT) a ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa Executive Order (E.O.) 13224, wanda ya saka tsararan takunkumai kan ‘yan ƙasar waje da ake ganin sun aikata, ko kuma suna barazanar aikata ta’addanci da zai kawo barazana ga rayuwar Amurkawa ko ƙasar, ko ƙudirin ƙasar, ko tattalin arzikinta. An kuma saka shi cikin jerin takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙudiri mai lamba 1844 (2008) saboda shiga da kuma taimakawa ga ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya, da tsaron Somalia da ma dakarun kiyaye zaman lafiya. Bugu da ƙari, Adan na da alaƙa da ƙawayen al-Qaida irinsu al-Qaida a yankin Larabawa, da al-Qaida a yankin Musulmin Afirka.

 

Skip to content