Abdullahi Osman Mohamed

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai kan Abdullahi Osman Mohamed.

Mohamed wanda kuma aka sani da Engineer Ismail, shi ne babban ƙwararre mai haɗa bamabamai na ‘yan ta’addan al-Shabaab. Shi ne ke da alhakin tafiyar da sashen bamabaman al-Shabaab da kuma haɗa su. Kuma mai ba da shawara ne na musamman ga “sarkin” al-Shabaab, kuma jagoran sashen yaɗa labarai na al-Shabaab mai suna al-Kataib.

A ranar 17 ga watan Nuwamban 2020, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Mohamed a matsayin Ɗan Ta’adda na Musamman a Duniya (SDGT) a ƙarƙashin sashe na 1(a)(ii)(B) na Umarnin Shugaban Ƙasa Executive Order (E.O.) 13224.

Skip to content