Abdul Rahman Yasin

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Yammacin Duniya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na miƙo tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Abdul Rahman Yasin, wanda kuma aka sani da Abdul Rahman Said Yasin da Aboud Yasin. Yasin ya taimaka wa ɗan ta’adda Ramzi Yousef kai-tsaye wajen aiwatar da harin 1993 kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ko World Trade Center da turanci, wadda ke birnin New York City.

A ranar 26 ga Fabarairun 1993, Yasin ya raka Yousef zuwa Cibiyar Kasuwanci ta Duniya cikin wata mota maƙare da abubuwan fashewa, waɗanda suka jibge a wurin ajiye ababen hawa na ƙarƙashin ƙasa na cibiyar. Tashin bam ɗin ke da wuya, ya kashe mutum shida kuma ya raunata fiye da 1,000, sannan ya lalata dukiyar da ta kai dubun-dubata. Yasin ya gudu zuwa Iraq don kada a kama shi. Saboda rawar da ya taka a harin, an tuhume shi da aikata laifuka masu yawa a Amurka.

An haifi Yasin a Amurka, ya koma Iraq a shekarun 1960, sannan ya koma Amurka a 1992. Yana da fasfo na Amurka. Yana cikin jerin sunayen ‘ya ta’addan da FBI ta fi nema.

Skip to content