Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Abdelkarim Hussein Mohamed al-Nasser. Al-Nasser da ake zargi da kasancewa shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah), ana nemansa ne saboda rawar da ya taka a harin bam na 1996 kan ginin Khobar Towers da ke kusa da Dhahran a Saudiyya.
A ranar 25 ga watan Yunin 1996, mambobin Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah) suka tada bam da ke jikin mota a wurin ajiye motoci na ginin Khobar Towers, wani ruƙunin gidaje da sojojin Amurka ke zaune a ciki. Fashewar ta tarwatsa gini mafi kusa tare da kashe dakarun Amurka 19 da kuma wani ɗan Saudiyya, kuma ya raunata ɗaruruwan ‘yan ƙasashe da dama.
A ranar 21 ga Yunin 2001, wani rukunin masu taimaka wa alƙali ya gano laifin al-Nasser da wasu mutum 13 da ke da hannu a harin.
A ranar 12 ga watan Oktoba na 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Nasser matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon wannan ayyanawa, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Nasser taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da al-Nasser. Kazalika, yana cikin jerin sunayen ‘yan ta’addan da FBI suka fi nema.
