Abd al-Rahman al-Maghrebi

Kudu da Tsakiyar Asiya | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 7

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 7 don bayanai kan Muhammad Abbatay, wanda aka fi sani da Abd al-Rahman al-Maghrebi. Al-Maghrebi babban jagoran Al-Qa’ida (Al-Qa’ida – AQ) ne da ke zaune a Iran. Shi ne jagoran sashen yaɗa labarai na AQ mai suna al-Sahab na tsawon lokaci, kuma siriki ne da mai ba da shawara ga jagoran AQ Ayman al-Zawahiri.

Wasu takardu da aka samu bayan kashe shugaban AQ Usama bin Ladin a 2011 sun nuna cewa al-Maghrebi tauraro ne mai tasowa a ƙungiyar AQ tsawon shekaru. Al-Maghrebi ya yi aiki a matsayin babban jagoran AQ a Afghanistan da Pakistan tun 2012. Sakamakon matsin lamba na yaƙi da ta’addanci a ƙasashen duniya, ya koma Iran inda ya ci gaba da lura da ayyukan AQ a faɗin duniya. A matsayinsa na shugaban sashen yaɗa labarai na AQ, al-Maghrebi na tsara ayyuka tare da ƙawayen AQ.

A ranar 12 ga watan Janairun 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Maghrebi matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Maghrebi taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da al-Maghrebi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa AQ kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.

Skip to content