Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun kuɗi na ƙungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP).
Abbas Hamdan babban jagoran AQAP ne kuma shugaba a sashen harkokin kuɗinta.
Abin koyi ne a AQAP wanda ya dinga ɗaukar nauyin ayyukanta da kai hare-hare kan wuraren da suka haɗa da kadarorin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
