Dakarun Neman Sauya Hali na Musulunci (Islamic Revolutionary Guard Corps - IRGC)

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 15

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 15 don bayanai da za su kai ga lalata harkokin samun kuɗi Dakarun Neman Sauya Hali na Musulunci (Islamic Revolutionary Guard Corps – IRGC) da sauran dukkan rassanta, ciki har da IRGC-Qods Force (IRGC-QF). IRGC ta ɗauki nauyin ayyukan ta’addanci masu yawa a faɗin duniya. IRGC-QF na jagorantar ayyukan Iran a wajen ƙasar ta hanyar ƙawayenta, kamar Hamas, da Hizballah, da sauran ƙungiyoyi masu samun goyon bayan Iran a Iraq.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na ba da tayin lada don samun bayanai kan hanyoyin samun kuɗi na IRGC da IRGC-QF, rassanta ko kuma manyan hanyoyin samun kuɗi, da suka haɗa da:

  • Haramtattun harkokin kuɗi na IRGC, ciki har da cinikin man fetur;
  • Kamfanonin da ke yi wa IRGC hada-hada tsakanin ƙasa da ƙasa;
  • Cibiyoyi ko mutane da ke taimaka wa IRGC wajen kauce wa takukuman da aka saka mata na ƙasa da ƙasa;
  • Sahihan cibiyoyin kuɗi da ke yin kasuwanci da IRGC;
  • Yadda IRGC ke tura kuɗaɗe da kayayyaki ga ‘yan ta’adda da ƙungiyoyi barandarsu da ƙawaye;
  • Masu ba wa IRGC kyautar kuɗi ko kuma masu lalubo mata hanyar kasuwanci;
  • Cibiyoyin kuɗi ko kuma wuraren canjin kuɗi da ke yi wa IRGC aiki;
  • Kasuwanci ko kuɗaɗen zuba jari da IRGC ke juyawa ko kuma masu ba da su;
  • Kamfanonin da ke yin safarar kayan fasaha sakanhan tsakanin ƙasa da ƙasa a madadin IRGC;kuma
  • Haramtattun tsare-tsare da mambobin IRGC ke yi ko magoya bayanta, waɗanda suke sama wa ƙungiyar riba.

Rundunar da aka kafa ta a 1979 bayan juyin juya halin Iran, IRGC wani ɓangare ne na rundunar sojan Iran. Ta hanyar rundunarta ta dakarunta na Qudus Force, IRGC na taka rawa mafi muhimmanci a ayyukan Iran na aiwatar da shirin ta’addanci a faɗin duniya.

IRGC ta sha shiryawa da kuma taimaka wa ta’addanci a duniya. IRGC ce ke da alhakin kai hare-hare daban-daban kan Amurkawa da gine-ginen Amurka, ciki har da waɗanda suka kashe ‘yan Amurkar. IRGC ta taimaka wajen kai wa dakarun Amurka da na ƙawayenta hare-hare, da kuma kan ofisoshin jakadanci a Afghanistan da Iraq.

Ƙari a kan haka, IRGC ta yi garkuwa da mutane sannan ta tsare Amurkawa ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda da yawansu ke tsare a Iran yanzu haka.

IRGC ta shirya hae-haren ta’addanci masu yawa a faɗin duniya, a ƙasashe kamar Bahrain, Bosnia, Bulgaria, Germany, Kenya, Turkey, Amurka.

A ranar 15 ga Afrilun 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana IRGC a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A 2017, Sashen Bailtul-Malin Amurka ya ayyana IRGC matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima, saboda taimaka wa IRGC-QF. Sakamakon haka, an hana IRGC taɓa dukkan dukiyar ko kadarorida ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da IRGC. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa IRGC kayan aiki da gangan.

Skip to content