An kafa rusasshiyar Ƙungiyar 15 ga Mayu (15 May Organization) ta ta’addanci a 1979. Kungiyar ta yi yunƙurin kafa kasar Falasɗinawa ta hanyar kashe ‘yan Isra’ila da Amurkawa da kuma lalata kadarorin Isra’ila da Amurka a fadin duniya. Ƙungiyar 15 May (15 May Organization) ta ɗauki alhakin hare-hare masu yawa, ciki har da harin bam a kan jirgin Pan Am 830 a 1982 da ya kashe wani fasinja mai shekara 16 da kuma raunata wasu 16.
