Ankararwa Kan Sirri
Mun gode da kuka yarda ku shiga shirin Lada Don Adalci. Mun duƙufa wajen kare bayananku da kuma haƙƙinku na a tsare bayananku.
Wannan ankararwar na bayyana yadda za mu iya yin amfani da bayananku idan kuka:
- Ziyarci shafinmu a adireshin https://38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips
- Hulɗa da mu ta wasu makamantan hanyoyi – ciki akwai kasuwanci ko taruka
Cikin wannan ankararwar kan adana sirri, idan muka ce:
- “Dandalin Yanar Gizo,” muna nufin kowane shafi mallakarmu da ke haɗe da ko kuma yake magana a kan wannan ankarawar
- “Ayyuka,” muna nufin shafin dandalin yanar gizonmu, da sauran ayyuuka da suka haɗa da talla da wasu taruka
Manufar wannan ankararwar ita ce don mu yi muku bayani ƙarara daidai gwargwado kan bayanan da muke karɓa, da yadda muke amfani da su, da kuma haƙƙin da kuke da shi game da su. Idan akwai wani sharaɗi da ba ku amince da shi ba a wannan ankararwar kan adana sirri, muna roƙonku da ku dakatar da amfani da kayayyakinmu nan take.
Muna roƙon ku ku karanta wannan bayanin bisa ankarawa kan sirri cikin natsuwa, saboda zai taimaka muku wajen fahimtar abin da muke yi da bayananku da muke karɓa.
Bayanan da Ake Karɓa Kai-Tsaye
A taƙaice: Wasu bayanan – kamar adireshinku na intanet (IP address) da/ko siffar na’urarku – ana karɓar su kai-tsaye idan kuka ziyarci shafinmu na intanet.
Muna karɓar wasu bayanai kai-tsaye idan kuka ziyarci shafin, ko kuka yi amfani da shi, ko kuma kuka zagaya a ciki. Waɗannan bayanan ba sa nuna wasu abubuwa na musamman game da ku (kamar suna ko hanyar tuntuɓa), amma za su iya ƙunsar siffar na’urarku kamar adireshin IP, da na manhajar shiga intenet (browser), da samfurin tsarin kwamfutarku (operating system), da harshen da kuka zaɓa, da adireshi-adireshin da kuka aika, da sunan na’ura, da ƙasa, da wurin da kuke, da kuma bayani kan lokaci da yadda kuke amfani da shafinmu, da sauran bayanai. Ana buƙatar waɗannan bayanan ne kawai don tsaro da kuma ayyukan shafinmu, da kuma ƙididdiga da muke yi da haɗa rahotanni.
Kamar sauran harkoki, muna kuma karɓar bayanai ta hanyar cookies da fasahohi irinsa.
Bayanan da muke karɓa sun ƙunshi:
- Bayanan Amfani da Gudanarwa: Bayanan amfani da gudanarwa na da alaƙa da yin amfani da gano matsala da kuma yadda na’urorinmu ke karɓar bayanai kai-tsaye idan kuka shiga shafinmu, wanda kuma muke ajiyewa rumbunmu. Ya danganta da yadda kuke mu’amala da mu, bayanan wannan rumbun za su iya ƙunsar adireshin IP, da bayanan na’ura, da nau’in manhajar shiga intanet (browser) da kuma ayyukanku a shafin (kamar rana da lokacin amfani da shafin, da shafuka da kuma fayil-fayil da kuka duba, abubuwan da kuka nemi ƙarin bayani akan su da sauran abubuwan da kuka yi kamar nau’in abin da kuka yi amfani da shi), bayanan abin da na’urarku ta aiwatar (kamar ayyukanta, da miƙa rahotannin kuskure (wani zubin ana kiran su ‘saƙonnin hatsari’ ko ‘crash dumps’ da turanci) da kuma saiti na’urar).
- Bayanan Na’ura: Muna karɓar bayanan na’ura kamar na kwamfutarku, da waya, da babbar waya (tablet), da sauran na’urorin da kuke amfani da su wajen shiga shafin. Ya danganta da na’urar da kuke amfani da ita, bayanan na’urar za su iya ƙunsar adireshin IP (ko layin proxy) lambobin da ke fayyace manhaja, da wuri, da nau’in manhajar shiga intanet (browser), da samfurin kayan aiki, da kamfanin da ke samar da layin intanet, da kuma sunan kamfanin da ya ƙera wayarku, da samfurin kwamfuta, da bayanan tsarin na’ura.
- Bayanan Wurin da ake: Muna karɓar bayanan wuri, kamar bayanan inda na’urar da kuke amfani da ita take, wanda ka iya yin daidai ko akasin haka. Yawan bayanan da muke tatsa ya danganta da nau’in na’urar da kuke amfani da ita wajen shiga shafin da kuma tsarinta. Misali, za mu iya yin amfani da fasahar GPS da sauran fasahohi don karɓi bayanin wurin da kuke (ta hanyar amfani da adireshin IP naku). Za ku iya hana mu karɓar waɗannan bayanan ta hanyar dakatar da mu daga samun su ko kuma ku kashe maɓallin gane wurin da kuke (location settings) a kan na’urarku. Sai dai kuma a kula, idan kuka zaɓi ku hana mu bayanan ba lallai ne ku iya amfani da wasu kayayyakin ba.
Ta Yaya Muke Amfani da Bayananku?
Muna amfani da bayanan da muka karɓa don gudanar da wasu harkokin kasuwanci daban-daban kamar haka.
Za mu iya yin amfani da bayananku wajen gudanar da abubuwa kamar haka:
- Don kare ayyukanmu. Za mu iya yin amfani da bayananku wajen yunƙurinmu na kare shafinmu da ba shi tsaro (misali, don bin diddigin zamba da yin rigakafi.)
- Don tabbatar da bin ƙa’idojinmu, da sharuɗa, da tsare-tsare wajen bin dokoki da kuma bin umarnin hukumomi.
- Don kammala da kuma taimaka wa ayyukan da ake cikin gudanarwa
- Don jagorantar da kuma kula da shafin
- Don gudanar da bincike da samar da ci gaba
- Don gudanar da binciken-binciken da hukuma ta amince da shi
Ko Muna Amfani da Cookies da Sauran Fasahohin Bin Diddigi?
A Taƙaice: Za mu iya amfani da cookies da sauran fasahohin bin diddigi (kamar web beacons da pixels) don karɓa ko ajiye bayanai.
Cookies da sauran fasahohi irinsa za su iya taimaka mana wajen gane ku kai-tsaye idan kuka sak dawowa shafinmu ko kuma manhaja. Cookies kan taimaka mana wajen tantance yadda ake tururuwa a shafin, da inganta shafin da kuma yin hasashen wadanne kayayyaki ne aka fi so. Za kuma mu iya yin amfani da waɗannan bayanai wajen tallata wasu kayayyaki na musamman ga masu amfani da su, waɗanda alamu suka nuna sun fi sha’awar sha’awar wani ɓangare.
Ta Yaya Muke Tsare Bayananku?
A Taƙaice: Muna da zimmar kare bayananku ta hanyar tsarawa da kuma ɗaukar matakan tsaro.
Matakai Kan Harkokin Kada-a-Bi-Diddigi
Sanarwa Ga Mutanen da Ke Shiga Wannan Shafin Dadalin Yanar Gizon Daga Wajen Amurka
Muna iko tare da kula da ayyukanmu ne daga Amurka, mazauna Amurka ne ke iya samun su, sannan kuma babu wata dokar wata jiha da ke kanmu, ko ƙasa, ko yanki, sai ta Amurka kawai. Za a iya amfani da kuma ajiye da duk wani bayani da kuka bayar ta hanyar amfani da kayayyaki, ko aika shi tare da samun sa a cikin Amurka da wasu ƙasashe, waɗanda ba lallai su ba da tsaro yadda ya kamata ba kan bayaananku irin na ƙasar da kuke zaune. Idan ba kwa so bayanan rayuwarku su bar ƙasarku, muna roƙonku da kada ku ba wa Lada Don Adalci kuma kada ku yi amfani da shafinmu na intanet. Da zarar kun ba wa Lada Don Adalci bayanan rayuwarku, kenan kun amince ƙwarai da gaske cewa za a iya kai bayanan naku Amurka.
Shirin Lada Don Adalci ko kuma masu yi masa wasu ayyuka ka iya aika bayanan rayuwarku daga Da’irar Tattalin Arziki ta Turai wato European Economic Area (EEA) zuwa wasu ƙaasashe, waɗanda har yanzu Hukumar Turai ba ta amince cewa wasu daga ciki za su iya samar da cikakken tsaro ba kan bayanan yadda zai dace da tsarin EEA. Idan a tura zuwa ƙasashen da ba sa buƙatar tsari kamar na EEA, Lada Don Adalci na amfani da tsare-taren shari’a don kare bayanan rayuwarku, ciki har da dokokin ƙulla yarjejeniya da kuma tabbaci a rubuce daga kamfanonin da ke samar da layi.
Adireshi Zuwa Wasu Shafukan
Dokar Zamba ta Intanet
Tsarin Ankarawa kan Sirri na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka
Yadda Za Ku Tuntuɓe Mu
Idan kuna da tambayoyi game da tsarinmu na ankarawa kan sirrin ko amfani da bayanai muna maraba da tsokaci. Za a iya samun kundin bin dokokin tsarin adana sirri a Privacy Impact Assessments (PIA) da and Systems of Records Notices (SORN). Don samun ƙarin bayani game da Tsarinnmu na Ankarawa kan Sirri, muna roƙonku da ku tuntuɓe mu a [email protected] ko kuma a aiko mana imel a:
Office of Global Information Services
Privacy Office – A/GIS/PRV
State Annex 9
U.S. Department of State
Washington, DC 20006
