Harin Bam Kan Jirgin TWA Flight 840

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Turai da Eurasia

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam a kan jirgin sama na TWA Flight 840. A ranar 2 ga watan Afrilun 1986, wani bam ya tashi a cikin jirgin TWA Flight 840 lokacin da yake kan hanyarsa daga birnin Rome zuwa Athens na Girka. Fashwar ta kashe Amurkawa huɗu, har da wata jaririya ‘yar wata tara da haihuwa da mahaifiyarta da kuma kakarta, waɗanda dukansu suka fice daga cikin jirgin. An jikkata wasi fasinjan biyar. Cikin wata sanarwa da aka fitar daga Beirut, ƙungiyar Arab Revolutionary Cells ta ɗauki alhakin kai harin.

Skip to content