Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 3 don bayanai da za su kai ga daƙile ko kuma shawo kan ta’addanci a kan duk wani Ba’amurke ko kuma dukiya da ke da alaƙa da difilomasiyyar Amurka. Duk wanda ya ba da rahoto sahihi kan wani hari da aka shirya kaiwa ko kuma wanda aka kai a baya kan harkokin difilomasiyyar Amurka zai iya cancantar samun wannan ladan. Harkokin difilomasiyyar Amurka sun ƙunshi ofisoshin jakadanci, gine-ginen ofishin, da kuma sauran ofisoshin wakilci a faɗin duniya.
