Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan aukuwar bam ɗin wasiƙa. Daga Disamban 1996 zuwa Janairun 1997, sau 16 ana ƙunshe bam a matsayin katin gaisuwa na lokacin hutu inda aka dinga isar wa mutane ta hanyar akwatin gidan waya a Amurka da Birtaniya.
Daga cikin waɗannan bam na wasiƙa, an karɓi 13 a ofisoshin jaridar al-Hayat da ke New York City, da Washington D.C. da kuma Landan. Bam ɗaya ya tashi a Laadan, inda ya jikkata mutum biyu. An gano sauran bam ukun a wani gidan yarin gwamnatin tarayyar Amurka da ke Leavenworth, Kansas.
Kowanne daga cikin bama-baman na ɗauke da hatimin birnin Alexandria na Egypt da kwanan watan 21 ga Disamban 1996, amma babu wanda ke ɗauke da adireshin inda suka fito. An saka bama-baman a wani farin ambulan ɗauke da adireshin da aka ɗauko daga kwamfuta da kuma sauran alamu.
