Garkuwa da Kevin Scott Sutay

Yammacin Duniya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 3

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 3 don bayanai kan sace Kevin Scott Sutay. A watan Yunin 2013 ƙungiyar Revolutionary Armed Forces of Colombia (FARC) ta sace Sutay, tsohon jami’in sojan Amurka, a kusa da birnin El Retorno da ke Colombia. Sutay ya sha yin tafiya a ƙasa don yawon buɗe-ido zuwa ƙasashen Tsakiya da Kudancin Amurka da dama
A ranar 19 ga watan Yuli na 2013, FARC ta fitar da sanawar tana ɗaukar alhakin sace shi sannan ta ce za ta sake Sutay saboda nuna kirkinta. Sai dai kuma, ba saki Sutay ba har sai 27 ga Oktoban 2013 lokacin da aka miƙa shi wakilai na gwamnatocin Colombia, da Cuba, da Norway da kuma mambobin ƙungiyar agaji ta International Committee of the Red Cross. Daga baya aka miƙa wa gwamnatin Amurka Sutay a Bogota, Colombia inda aka kai shi Amurka daga baya.

Skip to content