Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan harin da aka kai wa Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi a Benghazi na Libya. A ranar 11 zuwa 12 na 2012, Amurkawa huɗu – Jakadan Amurka a Libya John Christopher Stevens, da Jami’in Gudanarwa Sean Smith, da Ƙwararren ka Harkokin Tsaro Glen Anthony Doherty, da Tyrone Snowden Woods – aka kashe a wani harin ta’addanci kan Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi da Ginin Amurka a Benghazi na Libya. ‘Yan ta’adda sun kai hare-hare har da kunna wuta, da amfani da makamai masu sarrafa kansu. Da makamin roka a kan gine-ginen biyu, da kuma kai hari kan sojojin Amurka da ke kai ɗauki tsakanin wuraren. Ƙari a kan haka, hare-haren sun ji wa dakarun Amurka biyu mummunan rauni, suka raunata ‘yan kwangilar tsaro na Libya uku, sannan ya jawo lalata wuraren da kuma daina amfani da su.
An haifi Jakada John Christopher Stevens mai shekara 52 a arewacin California, kuma ya fara aiki da Ofishin Ƙasashen Waje a 1991. Jakada Stevens ya yi aiki da ofisoshin ƙasar waje da yawa kuma shi ne Mataimakin Shugaban Jakadanci a Libya daga 2007 zuwa 2009. Daga Maris ɗin 2011 zuwa Nuwamban 2011, Jakada Stevens ya yi aiki a matsayin Wakili na Musamman a Majalisar Riƙon Ƙwarya ta Libya, kuma ya isa birnin Tripoli a watan Mayun 2012 a matsayin Jakadan Amurka a Libya. Kafin ya fara aiki da Ofishin Ƙasashen Waje, Jakada Stevens lauyan ƙasa da ƙasa ne a birnin Washington, D.C. Ya koyar da harshen Ingilshi a mastayin ɗan sa-kai na Peace Corps a Moroco daga 1983 zuwa 1985. Sakatariyar Harkokin Waje Hillary Rodham Clinton ta bayyana Jakada Stevens a matsyain “jajirtacce mutumin kirki, ƙwararren jami’in difilomasiyya, kuma gwarzon Amurka”.
An haifi Sean Smith mai shekara 34 a San Diego, California, kuma ya shiga sojan sama a 1995, inda ya yi aiki a matsayin mai gudaar da sadarwa ta rediyo, kuma mai muƙamin saja. Smith ya fara aiki da Ofishin Ƙasashen Waje a 2002 a matsayin Jami’in Yaɗa Labarai, kuma ya yi aiki a ofisoshin ƙasashen waje da dama, ciki har da Baghdad, da Pretoria, da Montreal, da The Hague. Smith ya yi balaguro zuwa Benghazi a Satumban 2012 don ba da taimako a ɓangaren sadarwa ga Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi.
Glen Anthony Doherty mai shekara 42, an haife shi a Winchester, Massachusetts kuma an ɗauke shi a matsayin sojan ruwa a na rundunar Navy SEAL a 1995, inda ya yi aiki a Iraq da Afghanistan. Kafin ya zama sojan ruwa, Doherty ya yi aiki a matsayin mai koyar da sulu, ya je makarantar koyon tuƙin jirgi, kuma ƙwararren mai ba da taimakon lafiya ne da tuƙin jirgi. A 2005, Doherty ya fara aiki matsayin ɗan kwangilar tsaro yana ba wa jami’an Amurka tsaro a ƙasashen waje. Doherty ya je Benghazi a Satumban 2012 don ba wa jami’an Amurka tsaro.
An haifi Tyrone Snowden Woods mai shekara 41 a Portland, Oregon kuma ya shafe shekara 20 a matsayin Navy SEAL, inda ya yi aiki da tawaga masu yawa a Somalia, da Iraq, da Afghanistan. Kazalika, Woods tsohon ma’aikacin jinya ne. A 2010, Woods ya fara aiki a matsayin ɗan kwangilar tsaro, yana ba wa jami’an Amurka tsaro a ƙasashen waje Ya yi aiki a faɗin duniya wajen ba wa jami’ai tsaro. Woods ya je Benghazi a Satumban 2012 don ba wa jami’an Amurka tsaro.
