Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin 1999 a kan ‘yan yawon buɗe-ido a Bwindi Park da ke Uganda.
A ranar 1 ga watan Maaris na 1999, mambobin ƙungiyar Sojojin ‘Yanta Ruwanda (Liberation Army of Rwanda – ALIR) suka kai hari kan masu yawon bude-ido da ɗan jagoransu a Bwindi Impenetrable National Park da ke Uganda. An kai wa tawagar hari, aka yi garkuwa da su, sannan aka tilasta musu balaguro zuwa ƙasar Jamhuriyar Dimokurɗiyyar Congo. An ƙona wani ɗan Uganda mai suna Paul Ross Wagaba da ransa. Takwas daga cikin mutanen, ciki har da Amurkawa Susan Miller da Robert Haubner, an yi musu duka har suka mutu.
Jagoran harin ya ba wa waɗanda suka tsira wani rubutaccen saƙo cewa harin wani saƙo ne ga Amurka da sauran ƙasashe don su daina goya wa gwamnatin Ruwanda baya.
