Hari Kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da Pentagon (9/11)

Yammacin Duniya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 25

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 25 don bayanai kan harin 11 ga Satumban 2001 kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ginin Pentagon. ‘Yan ta’adda 19 ne da ke da al-Ka’ida (AQ) suka yi garkuwa da jiragen fasinja huɗu da ke kan hanyar zuwa california daga filayen jirgi uku da ke gabashin Amurka. ‘Yan ta’addan sun afkar da jirgi biyu kan hasumiyar ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke Birnin New York, shi kuma na ukun a kan Pentagon da ke Arlington, Virginia. Jirgi na huɗu ya afka a kusa da Shanksville, Pennsylvania yayin da fasinjoji suka yunƙurin yaƙar masu garkuwar. Jumilla, hare-haren sun kashe mutum kusan 3,000 ‘yan ƙasashen duniya daban-daban. Shugaban AQ da aka kashe, Usama bin Ladin, ya ɗauki alhakin shiryawa da kma ƙaddamar da waɗannan hare-hare a wani saƙon bidiyo bayan faruwarsu.

Jirage biyun farko da suka taso daga filin jirgi na Boston Logan International Airport, an yi garkuwa da su sannan aka faɗo da su kan manyan hasumiyar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a Birnin New York. Ƙarfin jiragen da kuma wutar da ta tashi sakamakon man jirgi sun lalata ginin har sai da ya ɗaiɗaice. Hari kan tagwayen ginin ya halaka mutum fiye da 2,600.

Jirgi na uku da ya tashi daga filin jirgi na Washington Dulles International Airport, an ƙwace shi kuma aka faɗo da shi kan ginin Pentagon minti 30 bayan na biyu ya faɗa kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya. Lamarin ya sa dukkan fasinjojin sun mutu, 125 a cikin ginin, kuma ya yi mummunar ɓarna ga ginin.

Jirgi na huɗu ya tashi daga filin jirgi na Newark International Airport, kuma da alama an so a faɗo da shi kan ginin Capitol ko kuma Fadar White House. Sai dai, fasinjojin da ke ciki sun yaƙi ‘yan ta’addan wajen karɓe iko da jigin. Saboda bajntar waɗannan ‘yan ƙasa, ‘yan ta’addan ba su cimma burinsu ba inda jirgin ya faɗo a kusa da Shanksville, Pennsylvania ya kashe dukkan mutum 40 da ke cikinsa.

Waɗannan hare-hare, su ne mafiya muni a Amurka daga wata rundunar ƙasar waje tun bayan Pearl Harbor a 1941.

Skip to content