Duran Kalkan

Turai da Eurasia

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 3

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan uku don samun bayanai kan Duran Kalkan, wani babban jagoran Jam’iyyar Ma’aikata ta Ƙurdawa (Kurdistan Workers Party – PKK), wanda aka sani kuma da Kongra-Gel. Amurka ta ayyana PKK a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO). Kalkan mamba ne a Kwamatin Gudanarwa na PKK kuma shi ne ke da alhakin kai harin da ya kashe sojojin Turkiyya bakwai a Disamban 2009.

Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Kalkan a matsayin Ɗan Sumogar Ƙwayoyi bisa Dokar Ayyana Ɗan Sumogar Ƙwayoyi na Ƙasar Waje wato Foreign Narcotics Kingpin Designation Act (Kingpin Act) ranar 20 g watan Afrilu na 2011.

Skip to content