Katse hanyoyin kudaden ISIS a Afirka ta Yamma

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara | Na Duniya gaba ɗaya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Shirin “Rewards for Justice” (Bada Tukuici don Adalci) zai bayar da tukuicin da zai kai har dala miliyan 10 don samun bayanan da zasu taimaka wajen katse hanyoyin samar da kudin kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS a Afirka ta Yamma (ISIS-WA).

Kungiyar dai, wadda an kafa ta ne can farko a arewa maso gabashin Najeriya, tana gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi na kasashen Kamaru, Chadi, Nijar, da Najeriya. Ana imanin cewa kungiyar ISIS-WA tana tara daruruwan dubunnan daloli kowane wata ta hanyar karbe kudi ko amfanin ayyukan noma da kamun kifi a yankin, da kuma sace mutane farar hula da tilasta musu biyan kudi . ISIS-WA ta kuma dogara da samun gudummawa, da hidimar kuɗi daga masu ba ta tallafi a duniya, kuma an yi imanin cewa tana samun kudade daga jagororin babbar kungiyar ISIS ta hanyar masu jigilar kuɗi, da kafofin hawala, da kudaden yanar gizo, da cibiyoyin hada-hadar kudi.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka zata bayar da tukuici don samun bayanan da zasu taimaka wajen katse hanyoyin samun kudin shiga da dabarun hidimar kudin ISIS-WA, wandanda suka hada da:

  • Bayar da gudummawar kuɗi ga ISIS-WA ta hanyar masu ba da tallafi and masu samar da lamunin kuɗi,
  • Manyan harkokin kudi ta hanyar cibiyoyin hada-hadar kudi da wuraren canji da aika kudade da ISIS-WA ke cin gajiyarsu,
  • Harkokin kasuwanci ko saka hannun jari mallakin ko karkashin ikon ISIS-WA ko masu sarrafa mata kudi,
  • Kamfanonin bayan fage da ke da alaka da ISIS-WA ko da ke gudanar mata da harkokin kuɗi,
  • Shirye-shiryen makirci da hadin kan mambobi da magoya bayan ISIS-WA waɗanda amfana wa kungiyar da kudade,
  • Haramtattun harkokin kudin da ISIS-WA ke yi,
  • Harkoki tsakanin hukumtattun cibiyoyin hada-hadar kudi da ISIS-WA, ko
  • Samar da kudade da kayayyaki daga ko zuwa ga ma’aikatan WISIS-WA.

An kafa ISIS-WA a shekarar 2015, lokacin da ISIS ta amince da mubaya’ar Boko Haram, wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke Najeriya, sanan ISIS ta kaddamar da Boko Haram a matsayin ISIS-WA. ISIS-WA tana gudanar da ayyukan ta’addanci da sauran munanan ayyuka a Afirka ta Yamma, ta yi watsi da tsarin iyakokin kasashe, tana yunkurin zubar da mutuncin gwamnatocin yankin, da nufin maye gurbinsu da daula nau’in ISIS. A matsayinta ta daya daga cikin manyan rassan ISIS masu karfi, ISIS-WA tana aikata sace-sacen mutane, da hare-hare kan jami’an gwamnati da jami’an tsaro da mutane farar hula. Don yin hakan, ISIS-WA amfani da kananan bindigogi, da kayan aikin sojoji da ta kwato, da abubuwa masu fashewa (wadanda mutane ke dauke da su, ko wandanda ke kan abin hawa, ko wandanda aka dorawa dabba, ko wadanda aka binne), da kuma kwanton bauna.  ISIS-WA ta mamaye yankuna da yawa kuma ta sa miliyoyin mutane gudun hijira a yankin.

A ranar 28 ga watan Fabrairu, 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-WA a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasashen waje a karkashin aya ta 219 ta dokar shige da fice da zama dan kasa, wadda aka yi wa gyaran fuska. Kafin nan, a ranar 27 ga Fabrairu 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-WA a matsayin gungun ta’adda na musamman dangane da doka ta 13224, wadda aka yi wa gyaran fuska. A sakamakon haka, an dakile duk dukiyoyin ISIS-WA da duk kaddarori ko gajiyarta a ƙarƙashin dokokin Amurka, kuma a akasari, an hana ‘yan ƙasar Amurka ma’amala da kasuwanci da ISIS-WA. Bai wa ISIS-WA akan sani, ko yin ƙoƙarin ko makarkashiyar samar mata da tallafin kayan aiki ko kudade ya kasance aikata laifi.

Skip to content