Subayt bin Harith

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP).

Subayt bin Harith babban jagora ne a AQAP kuma mamba a majalisar shura ta ƙungiyar.

Wanda aka sani da Abu Ghazwan al-Hadrami, bin Harith ya kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar kuma ya tsara tafiye-tafiyen mayaƙa daga ƙasashen waje zuwa Yemen.

Skip to content