Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga toshe hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Hamas, wadda kuma ake kira da Harakat al-Muqawama al-Islamiya.
Abdelbasit Hamza Elhassan Mohamed Khair mai taimaka wa Hamas ne da kuɗi a Sudan, wanda kuma ya jagoranci kamfanoni da dama a harkokin kasuwancin ƙungiyar. Yana da alaƙa daɗaɗɗiya da al-Qaida da kamfanonin Usama bin Laden na Sudan.
Yana cikin waɗanda suka tura wa Hamas dala miliyan 20, har da tura wa jagoran kasuwancin ƙungiyar kuɗi kai-tsaye, da ma Mahir Jawad Yunis Salah wanda aka ayyana shi a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT).
Daga cikin ayyukan halasta kuɗin haram da da Hamza ke yi wa Hamas akwai kamfanin gine-gine a Sudan Al Rowad Real Estate Development, da Zawaya Group for Development and Investment Co. LTD, da Larrycom for Investment Company, har ma da Zawaya Group for Development Investment Sociedad Limitada da ke ƙasar Spain. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana duka huɗun a matsayin ‘yan ta’addan duniya na musamman.
A ranar 18 ga watan Oktoba na 2023, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Hamza a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT) bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Hakan ya sa an toshe duk wata dukiyar mutum da kuma kamfanoni da suka aikata ta’addanci, ko suke barazanar aikatawa. Ƙari kan haka, umarnin ya bai wa gwamnatin Amurka damar riƙe dukiyar mutum ko kamfanoni da ke taimakawa, ko yin aiki, ko alaƙa da ‘yan ta’adda ko ƙungiyoyin ta’addanci da aka ayyana a ƙarƙashin umarnin, har ma da rassansu, da masu shige musu gaba, da wakilansu, da abokan aikinsu.
