Muhammad Ahmad ‘Abd Al-Dayim Nasrallah

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga dakatar da hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Hamas, wadda kuma ake kira Harakat al-Muqawama al-Islamiya.

Muhammad Ahmad ‘Abd Al-Dayim Nasrallah ya daɗe a matsayin mamban Hamas da ke zaune a Qatar, kuma yake da alaƙa mai ƙarfi da Iran. Yana cikin masu aika miliyoyin dala ga Hamas, cikinsu har da sashen soja na Hamas Izz al-Din al-Qassim Brigades.

A ranar 18 ga watan Oktoba na 2023, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Nasrallah a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT) bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Hakan ya sa an toshe duk wata dukiyar mutum da kuma kamfanoni da suka aikata ta’addanci, ko suke barazanar aikatawa. Ƙari kan haka, umarnin ya bai wa gwamnatin Amurka damar riƙe dukiyar mutum ko kamfanoni da ke taimakawa, ko yin aiki, ko alaƙa da ‘yan ta’adda ko ƙungiyoyin ta’addanci da aka ayyana a ƙarƙashin umarnin, har ma da rassansu, da masu shige musu gaba, da wakilansu, da abokan aikinsu.

Skip to content