Shirin Lada Don Adalci na miƙo tayin dala miliyan 10 don neman bayanai kan duk wani mutum da ke da hannu a harin da aka kai Asasey Hotel da ke Kismayo, Somalia.
A ranar 12 ga watan Yulin 2019 wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a jikin wani abin hawa a otel ɗin na Asasey da zimmar bai wa sauran ‘yan ta’addan al-Shabaab damar shiga ginin. Maharan sun kashe mutum 26, ciki har da Amurkawa biyu kuma suka raunata wasu 56. Jami’an tsaron Somalia sun yi nasarar kashe huɗu daga cikin maharan.
Al-Shabaab ce ke da alhakin kai hare-haren ta’addanci a Kenya, da Somalia, da kuma maƙwabtan ƙasashe da suka kashe dubban mutane, cikinsu har da Amurkawa. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya (FTO) da kuma Ƙungiyar Ƙa’addanci ta Musamman a Duniya (SDGT) a watan Maris na 2008. A watan Afrilun 2010, shi ma kwamatin takunkumi kan Somalia na kwamatin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana al-Shabaab a sakin layi na 8 na ƙudiri mai lamba 1844 (2008).
