Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai kan Ali Mohamed Rage. Rage babban jagora ne kuma kakakin ƙungiyar al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje. Rage ya shirya hare-haren ta’addanci da yawa a Somaliya da Kenya a madadin ƙungiyar. Ya zama babban kakakin al-Shabaab a watan Mayun 2009. A ranar 6 ga watan Agustan 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana shi a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya a ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima.
