Hari a Manda Bay Airfield, Kenya

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Shirin Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don neman bayanai kan Maalim Ayman da kuma duk wanda ke da hannu a harin ta’addanci na ranar 5 ga watan Janairun 2020 a Manda Bay Airfield da ke Kenya. Manda Bay sansani ne na sojojin Kenya da dakarun Amurka ke amfani da shi wajen horas da sojojin ƙasashen Afirka ta Gabas da ba da taimakon wajen yaƙi da ta’addanci, kai agaji a wuraren rikici, da kuma kare muradan Amurka a yankin.

A wani harin tsakar dare, mayaƙan al-Shabaab sun harba makamai kan kayayyakin Amurka da Kenya da ke cikin sansanin, sannan suka harba gurneti (RPG) da ƙananan makamai a kan filin jirgi na Manda Bay Airfield da ke maƙwabtaka. Mutum biyu matuƙa jirgi na haya, ‘yan Amurka, daga Ma’aikatar Tsaro ta Amurka (DoD), aka kashe lokacin da makamin RPG ya sauka kan jirginsu a kan titin jirgi na filin jirgin. Wani ma’aikacin haya na DoD, shi ma Ba’amurke, ya tsira daga fashewar da ta afku amma da mummunan rauni. An kashe wani ƙwararren sojan Amurka da ke ba da hannu a musayar wutar da ta biyo bayan harin, aka kuma raunata wasu sojojin Amurka biyu.

Cikin wani bidiyo da al-Shabaab ta saki daga baya a shafin dillancin labarai na Shahada News Agency, wani mai magana da yawun ƙungiyar ya ɗauki alhakin kai harin.

Maalim Ayman, wani jagoran rundunar Jaysh Ayman ta al-Shabaab mai kai hare-hare ta’addanci a Kenya da Somaliya, shi ne ya tsara harin na Janairun 2020. A watan Nuwamban 2020, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Ayman a matsayin Babban Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Dokar Umarnin Shugaban Ƙasa na 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima.

Al-Shabaab – mai alaƙa da al-Ƙa’ida a Gabashin Afirka – ita ce ta kai harin ta’addanci da dama a Kenya, da Somaliya, da kuma maƙwabtansu tare da kashe dubban mutane, ciki har da Amurkawa. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya a watan Maris na 2008. A watan Afrilun 2010, Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC) ya sake ayyana al-Shabaab a ƙarƙashin yarjejeniya ta 1844 (2008).

Skip to content