Ali al-Sha’ir

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Ali al-Sha’ir na aiki ne a matsayin manajan ofishin mai ɗaukar nauyin Hizballah, Hasib Muhammad Hadwan, kuma ya yi ta karɓar tallafin kuɗi a madadin Hizaballah tun daga shekarar 2000. Daga cikin ayyukansu, Ali al-Sha’ir da Hadwan na amfani da tsarin tura kuɗi na duniya wajen aika kuɗi zuwa Lebanon ta hanyar ɓoye manufarsu wadda ita ce ɗaukar nauyin ƙungiyar ta’addanci.

A ranar 17 ga watan Satumban 2021, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana al-Sha’ir matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Sha’ir taɓa duk wata dukiya da ya mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da al-Sha’ir. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.

Skip to content