Abdul Reza Shahla’i

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 15

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 15 don bayanai kan harkokin kuɗi, da gungun hulɗa, da abokan Abdul Reza Shahla’i, wanda kuma aka sani da ‘Yusuf Abu al-Karkh’ da Hajji Yusef. Shahla’i babban jami’i ne a Dakarun Tsaro na Neman Sauya Hali na Musulunci – Rundunar Qods (Islamic Revolutionary Guard Corps-Qods Force – IRGC-QF) ta ƙasar Iran da ke ayyuka a birnin Sanaa na Yemen. Shahla’i ya daɗe yana kai wa Amurkawa da ƙawayen Amurka hari a faɗin duniya.

Shahla’i ya tsara kisan sojojin ƙawance a Iraq, ya ba wa ‘yan Shia masu tsaurin ra’ayi makamai, sannan ya shirya harin ranar 20 ga Janairun 2007 a Karbala na Iraq, wanda ya kashe sojojin Amurka biyar tare da raunata wasu uku.

Matsayinsa na mai ɗaukar nauyi kuma babban jami’in IRGC, a 2011 ne Shahla’i ya biya kuma jagoranci shirin kashe jakadan Saudiyya a Amurka a birnin Washington D.C. Shahla’i ya kuma shirya wasu hare-hare a cikin Amurka. Da manufar tasa ta yi nasara, da kusan fararen hula 200 ne za a kashe a Amurka.

Daga baya kuma, a ranar 11 ga Oktoban 2011 Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Shahla’i matsayin Ɗan Ta’addan na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Daga baya kuma, a 2008 Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Shahla’i bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13438 saboda ya addabi zaman lafiyar Iraq da gwamnatin ƙasar. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an toshe duk wata dukiya ko kadarori mallakar Shahla’i waɗanda ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da shi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa IRGC kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Haka nan, Bahrain da Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) da Saudiyya da Birtaniya duk sun ayyana shi a 2018.

Skip to content