Malik Abou Abdelkarim

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Malik Abou Abdelkarim, wanda aka sani da Abd al-Karim ko Abu Abd al-Karim al-Tariqi. Abdelkarim babban jagora wasu mayaƙa ne na Al-Qa’ida a Yankin Musulman Maghreb (Al-Qa’ida in the Islamic Maghreb – AQIM), wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. 

A ƙarƙashin jagorancin Abdelkarim, tawagarsa na da makamai sannan sun yi garkuwa da mutane da kuma kai ƙananan hare-haren ta’addanci a faɗin Arewa da kuma Yammacin Afirka. An ruwaito Abdelkarim ya kashe wani tsoho ɗn Faransa a ya yi garkuwa da shi a Nijar a Yulin 2010. Wani hari da tawagar Abdelkarim ta kai a watan Yunin 2010 ya haddasa kisan jami’an tsaron Algeria 11.

Skip to content