Hari Bam Kan Sansanin Soja na Marine Corps Barracks

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don samun bayanai kan harin bam na 1983 da aka kai kan barikin sojan Amurka a Beirut na Lebanon. A ranar 23 ga watan Oktoba na 1983, wata motar bama-bamai ta tarwatse a wani ginin da Dakarun Ƙawancen Amurka da Faransa ke sansani a Lebanon a fillin jirgin sama na Beirut International Airport. Dakarun Ƙwancen sun je Lebanon ne a matayin wani ɓangare na dakarun ƙasa da ƙasa da ke kiyaye zaman lafiya. Harin ya kashe dakarun Amurka 241 sannan ya jikkata wasu 128. A ranar dai, an kashe dakarun Faransa 58 a irin wannan hari. An yi imanin Hizballah ce ta kitsa hare-haren tare a taimakon kuɗi daga Iran.

Skip to content