Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Muhammad Abdullah Khalil Hussain ar-Rahayyal, wanda aka sani da Khalil Antwan Iwan da Khalil Alid. Ar-Rahayyal da ake zargin mamba ne a Ƙungiyar Abu Nidal (Abu Nidal Organization) ta ta’addanci, ana nemansa saboda rawar da ya taka a garkuwa da jirgin Pan Am Flight 73 in Karachi, Pakistan ranar 5 ga Satumban 1986. Bayan tsare fasinjoji 379 da ma’aikatan jirgin tsawon awa 16, sai masu garkuwar suka fara harbi kan mai tsautsayi. Mutum 20 ciki har da Amurkawa biyu aka kashe sannan aka raunata fiye da 100.
Saboda rawar da ya taka a garkuwar, wani rukunin masu taimaka wa alkali a Amurka ya ce ar-Rahayyal na da laifi kuma yana cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema. Ana zaton ar-Rahayyal na zaune a Gabas ta Tsakiya.
