Muhammad Kawtharani

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan ayyuka da gungu da abokan Muhammad Kawtharani, wanda aka sani daJafar Kawtharani. Kawtharani babban jagoran dakarun Hizaballah ne a Iraq. Kawtharani ya karɓi ragamar wasu ƙungiyoyin siyasa na Iraq da ke ƙawance wasu ƙungiyoyin na Iran a hukmance, waɗanda tsohon janar ɗin Islamic Revolutionary Guard Corps general, Qasem Soleimani, ya shirya.

Kawtharani na tsara ayyuka tsakanin ƙungiyoyin da ba sa ƙarƙashin ikon gwamnatin Iraq da suka hana zanga-zanga ta ƙarfin tsiya, suka kai wa ofisoshin difilomasiyya hare-hare, sannan suka dinga aikata laifuka. A matsayinsa na mamba a Majalisar Siyasa ta Hizballah, Kawtharani ya faɗaɗa ayyukan Hizballah zuwa ba da horo, da kuɗaɗe, da taimakon siyasa da tallafi ga ƙungiyoyin ‘yan Shia na Iraq masu ta da ƙayar-baya. Kawtharani ya kuma taimaka wa masu tsattsauran ra’ayi tsallakawa Syria don taimaka wa gwamnatin Assad.

A ranar 22 ga Agustan 2013, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Kawtharani a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Kawtharani taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Kawtharani. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.

Skip to content