Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Sajid Mir wanda aka sani da Sajid Majid Chuhdri da Sajid Majid. Mir wanda babban mamba ne a ƙungiyar Lashkar-e-Tayyiba (LeT) ta ‘yan ta’adda a Pakistan, ana neman sa ne saboda rawar da ya taka a harin ta’addanci na Nuwamban 2008 a Mumbai, Indiya. Mir ne manajan harin na LeT, inda ya taka babbar rawa wajen shiryawa da aiwatarwa.
Daga ranar 26 zuwa 29 ga Nuwamban 2008, wasu mayaƙa 10 da LeT ta horar sun kai jerin hare-hare kan wurare da yawa a Mumbai na Indiya, inda suka kashe mutum 166. Amurkawa shida aka kashe lokacin da suka yi wa wurin ƙawanya tsawon kwana uku. Ben Zion Chroman, da Gavriel Holtzberg, da Sandeep Jeswani, da Alan Scherr, da Naomi Scherr, da kuma Aryeh Leibish Teitelbaum.
Mir ya kasance babban mamba a LeT tun daga kusan shekarun 2001. Daga 2006 zuwa 2011, Mir ne shugaban ayyukan LeT na ƙasashen waje kuma ya tsara hare-hare daban-daban a madadin ƙungiyar. An ruwaito cewa Mir ya haɗa baki don kai wa wani gidan jarida hari da ma’aikatansa a Denmark tsakanin 2008 zuwa 2009.
Saboda rawar da ya taka a hare-haren Mumbai, an gano laifin Mir a Amurka a Afrilun 2011. A ranar 30 ga watan Agustan 2012, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Mir a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon wannan ayyanawa, baya ga sauran abubuwa, an hana Mir taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Mir. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa LeT kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Mir na cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema. Ana kyautata zaton yana zaune a Pakistan.
