Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan garkuwa da kuma kisan Peter Kilburn. Kilburn ya kasance tsohon masani a ɗakin karatu na jami’ar American University of Beirut. A 3 ga watan Disamban 1984 aka ba da rahoton ɓacewarsa. Wata 16 bayan haka, an ga gawarsa tare da sauran wasu mutum biyu da aka kama. An harbe mutanen sannan aka yar da gawarwakinsu a kan duwatsun da ke gabashin birnin Beirut. Kilburn na cikin mutum 100, akasarinsu Turawa, da Hizballah da ƙawayenta suka yi garkuwa da su lokacin tashin hankalin Lebanon da ya ɗauki tsawon lokaci.
