Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Salman Raouf Salman, wanda aka sani da Samuel Salman El Reda da Salman Remal. Salman na jagorantar ayyukan ta’addanci na Hizballah a Yammacin duniya. Salman wanda jagora ne a rundunar tsaron ta waje a Hizaballa ta External Security Organization (ESO), an sha kitsa hari tare da shi a faɗin duniya. ESO ɓangare ne na Hizballah da ke da alhakin siryawa da tsarawa da ƙaddamar da hare-haren ta’addanci a wajen Lebanon. Babban muradin hare-haren shi ne lahanta Yahudawa da Amurkawa.
An gano Salman ne ya yi aiki a matsayin mashiryin harin bam na ranar 18 ga watan Yulin 1994 cibiyar Yahudawa ta Jewish Mutual Aid Society a birnin Buenos Aires. Fashwar da aka haddasa daga wata mota ta kashe mutum 85 tare da raunata wasu fiye da 300.
A ranar 19 ga Yulin 2019, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Salman matsayin Ɗan Ta’addan na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Salman taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Salman. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.
