Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Sami al-Uraydi, wanda aka sani da Abu Mahmud al-Shami. Al-Uraydi ya shiga shirye-shiryen kai harin ta’addanci kan Amurka da Isra’ila a baya. Al-Uraydi babban jami’in shari’a ne na ƙungiyar Hurras al-Din ƙawar al-Qa’ida kuma mamba a majalisar shura ta ƙungiyar. Hurras al-Din ya kuma kasance babban jami’in shari’a na al-Nusrah Front daga 2014 zuwa 2016, amma ya fita daga ƙungiyar a 2016.
