Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan Sayf al-Adl. Sayf al-Adl babban jagoran Al-Ka’ida (Al-Ka’ida – AQ) ne kuma mamba a majalisar shugabanni ta Majlis al-Shura. Al-Adl ya kuma jagoranci rundunar sojan AQ.
Wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya gano laifin Al-Adl a Nuwamban 1998 saboda hannunsa a harin bam na ranar 7 ga Agustan 1998 kan Ofishin Jakadancin Amurka a Dar es Salaam, Tanzania, da Nairobi, Kenya. Hare-haren sun kashe fararen hula 224 sannan suka raunata wasu fiye da 5,000.
Bayan hare-haren bam kan ofisoshin a 1998, al-Adl ya koma kudancin Iran kuma ya zauna ƙarƙashin kariyar rundunar Dakarun Neman Sauya Hali na Musulunci (Islamic Revolutionary Guard Corps – IRGC) na Iran. A watan Afrilun 2003, hukumomin Iran sun yi masa tare da wasu jagororin AQ ɗaurin talala.
A Satumban 2015, an saki al-Adl da wasu manyan shugabannin AQ daga gidan yarin Iran a matsayin musaya da wani jami’in difilomasiyyar Iran da AQ ta yi garkuwa da shi.
Al-Adl babban dakaren soja ne na Abu Musab al-Zarqawi, wanda ya kafa AQ a Iraq wadda daga baya ta zama Islamic State of Iraq and Syria (ISIS).
Tun farkon 1990, al-Adl da wasu jami’an AQ sun ba wa mayaƙan AQ horo da bayanan sirri da kuma ƙawayensu a ƙasashen Afghanistan, da Pakistan, da Sudan, ciki har da Jihadin Musulunci na Masar (Egyptian Islamic Jihad).
A 1992 da 1993, ya ba wa dakarun AQ horo da kuma mayaƙa ‘yan Somalia da suka yaƙi sojojin Amurka a Mogadishu lokacin rikicin Operation Restore Hope.
A matsayinsa na kanar a rundunar sojan Masar ta musamman a shekarun 1980, ya shiga yunƙurin hamɓarar da gwamnatin Masar. A 1987, an kama shi tare da wasu masu adawa da gwamnati bayan yunƙurin kashe ministan harkokin cikin gida. Hukumomi sun sake al-Adl sannan suka rage masa muƙami, wanda a 1989 ya je Afghanistan ya zama mai horar da mayaƙan AQ.
A baya, a ranar 23 ga watan Satumban 2001, an saka al-Adl cikin jerin Annex to Executive Order 13224, kuma daga baya yana iya fuskantar hukunci ƙarƙashin dokar saboda matsayinsa na Ɗan Ta’adda na Duniya. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Adl taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amur kawa yin hulɗar kuɗi da al-Adl. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa AQ kayan aiki da gangan. al-Adl na cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema.
