Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Jamal Saeed Abdul Rahim, wanda aka sani da Ali Al Jassem Fahd da Ismael. Rahim wanda ake zargi da shiga Ƙungiya Abu Nidal, ana nemansa ne saboda hannunsa a harin ranar 5 ga watan Satumba na 1986 da aka yi garkuwa da jirgin Pan Am Flight 73 a Karachi, Pakistan. Bayan tsare fasinjoji 379 da ma’aikatan jirgin tsawon awa 16, sai masu garkuwar suka fara harbi kan mai tsautsayi. Mutum 20 ciki har da Amurkawa biyu aka kashe sannan aka raunata fiye da 100.
Saboda hannunsa a garkuwar, wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya gano laifin Rahim kuma yana cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da FBI ta fi nema. Akwai yiwuwar Rahim na zaune a Gabas ta Tsakiya.
