Garkuwa da Jirgin TWA Flight 847

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Turai da Eurasia

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan garkuwa da jirgin sama na TWA Flight 847 a 1985. A ranar 14 ga Yunin 1985, ‘yan ta’adda suka karkatar da jirgin saman na TWA Flight 847 daga Athens zuwa Rome. Tsawon kwana 17 aka tilasta wa jirgin ya yi ta shawagi a saman Tekun Mediterranean ɗauke da fasinjoji 153 da ma’aikata daga Beirut zuwa Algiers, inda ya yi ta yin hakan kuma ya sauka Beirut har sau uku. A tsayawarsa ta farko a Beirut, masu garkuwar suka dinga dukan wani sojan Amurka Robert Stethem, sannan daga baya suka harbe shi.

A ranar 14 ga watan Nuwamban 1985, wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya ce Ali Atwa, da Mohammed Ali Hamadei, da Hasan Izz-al-Din na da hannu a harin. Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai kan Atwa, da Hamadei, da Izz-al-Din.

Skip to content