Ibrahim Ahmed Mahmoud al-Qosi

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 4

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 4 don bayanai kan Ibrahim Ahmed Mahmoud al-Qosi, wanda aka sani da Sheikh Khubayb al-Sudani da Mohammad Salah Ahmad. Al-Qosi ne shugaban Al-Ka’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.

Al-Qosi ya shiga AQAP a 2014, amma ya ci gaba da zama mamban al-Ka’ida (AQ) kuma ya yi wa marigayi Usama bin Ladin aiki kai-tsaye tsawon shekaru. An kama aal-Qosi Pakistan a watan Disamban 2001 kafin a mayar da shi gidan yari na Guantanamo Bay. Ya amsa laifi haɗa baki da AQ da kuma taimaka wa ta’addanci kafin 2010 a gaban wata hukumar soja. Amurka ta saki al-Qosi kuma ta mayar da shi Sudan a 2012 bisa wata yarjejeniya kafin fara shari’a.

Tun 2015, al-Qosi ya bayyana a kafofin ɗaukar mayaƙa na AQAP sannan ya dinga ƙarfafa gwiwar kai hari kan Amurka ta aikatawar mutum ɗaya kaɗai a kafofin farfaganda na yanar gizo. Ya yi aiki tare da tawagar shugabannin da ta taimaka wa tsohon shugaban AQAP marigayi Qasim al-Rimi.

Skip to content