Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam na ranar 31 ga watan Yulin 2002 a jami’ar Hebrew University da ke Birnin Ƙudus (Jerusalem). Mutum tara aka kashe ciki har da Amurkawa biyar, sannan aka raunata wasu 85 lokacin da bam ya tashi a wurin cin abinci na jami’ar Hebrew University. Maharan sun kai harin ne bisa umarnin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Hamas.
