Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Hasan Izz-al-Din, wanda aka sani da Ahmed Garbaya da Samir Salwwan. Ana neman Izz-al-Din da ake zargi da kasancewa mamban Hizballah saboda rawar da ya taka a garkuwa da jirgin sama na TWA Flight 847 a 1985.
A ranar 14 ga Yunin 1985, ‘yan ta’adda suka karkatar da jirgin saman na TWA Flight 847 daga Athens zuwa Rome. Tsawon kwana 17 aka tilasta wa jirgin ya yi ta shawagi a saman Tekun Mediterranean ɗauke da fasinjoji 153 da ma’aikata daga Beirut zuwa Algiers, inda ya yi ta yin hakan kuma ya sauka Beirut har sau uku. A tsayawarsa ta farko a Beirut, masu garkuwar suka dinga dukan wani sojan Amurka Robert Stethem, sannan daga baya suka harbe shi.
A ranar 14 g watan Nuwamban 1985, an gano hannun Izz-al-Din a shiryawa da taka rawa wajen aiwatar da garkuwar. A ranar 12 ga Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Izz-al-Din a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Izz-al-Din taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Izz-al-Din. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Izz-al-Din na cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da FBI ta fi nema. An yi imanin cewa yana Lebanon.
