Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 4 don bayanai kan Cemil Bayik. Bayik ɗan kwamatin gudanarwa ne, babban jami’i kuma wanda aka kafa Jam’iyyar Ma’aikata ta Ƙurdawa (Kurdistan Workers’ Party – PKK) da shi, wanda kuma aka sani da Konga-Gel. Amurka ta ayyana PKK a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO).
Ma’aikatar Harokin Wajen Amurka ta ayyana Bayik a matsayin Ɗan Sumogar Ƙwayoyi wato Specially Designated Narcotics Trafficker (SDNK) bisa Dokar Ayyana Ɗan Sumogar Ƙwayoyi na Ƙasar Waje ta Foreign Narcotics Kingpin Designation Act (Kingpin Act) ranar 20 ga watan Afrilun 2011.
