Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan A don bayanai kan harin jirgin USS Cole. A ranara 12 ga Oktoban 2000, wasu ‘yan ƙunar-baƙin-wake biyu suka kutsa wani ƙaramin jirgin ruwa cike da abubuwan fashewa kan USS Cole – wani jirgin ruwan yaƙi na sojan Amurka – a tekun Aden na Yemen, yayin da ya tsaya shan mai. Sakamakon fashewar ya haddasa wani wagegen rami a gefen jirgin, ya kashe mutum 17 sannan ya raunata wasu fiye da 30. Mambobin al-Qa’ida ne suka shirya harin, cikinsu akwai marigaya Jamal Ahmed Mohammed Ali al-Badawi da Fahd Mohammed Ahmed al-Quso.
