Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Zerrin Sari, wanda aka sani kuma da Fatma Gulten da Hale Melis. Sari, wani babban jagora ne a kungiyar Jam’iyyar ‘Yanta Al’umma (Revolutionary People’s Liberation Party/Front – DHKP/C ), wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje da ta kai hari kan gine-ginen gwamnatin Turkiyya da kuma dakarunta haɗi da wasu gine-ginen sojoji da na jakadancin Amurka a Turkiyya tun shekarun 1990. Burin DHKP/C shi ne dakile tasirin Amurka da NATO a Turkiyya da kirkiro ƙasarsu ta ‘yan gurguzu.
Duk da cewa an daure Sari a gidan yari saboda munanan ayyukanta, an sake ta a 2008 bayan rasuwar mijinta, Dursun Karatas, wanda aka kafa kungiyar DHKP/C da shi. Ta taka muhimmiyar rawa a hare-haren watan Maris din 2013 kan hedikwatar jam’iyyar siyasa ta the Justice and Development Party (AKP) da kuma kan ginin Ma’aikatar Shari’a ta Turkiyya dukkansu a birnin Ankara da ya raunata mutum ɗaya, da kuma harin 20 ga watan Satumban, 2013 kan hedikwatar ofishin ‘yan sandan Turkiyya da wani katafaren ginin ‘yan sanda a Ankara.
