Abdullahi Nowbahar

Kudu da Tsakiyar Asiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 2

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 2 don bayanai kan Abdullah Nowbahar. Nowbahar ƙwararre kan haɗa bam kuma abokin hulɗar Hezb-e Islami Gulbuddin (HIG), sannan mamba ne na sashen HIG mai haɗa bam da Saboor ke jagoranta. Nowbahar da Saboor ne kan gaba cikin waɗanda suka kai harin bam ranar 18 ga Satumban 2012 cikin mota kan wata bas da ke ɗauke da ma’aikatan Filin Jirgin Sama na Kabul a Afghanistan ‘yan ƙasar waje. Fashewar ta kashe mutum 12.

A ranar 10 ga Maris ɗin 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Nowbahar a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224. Sakamakon haka, baya ga sauran abubuwa, an hana Nowbahar taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Nowbahar.

Skip to content