Abdul Wali

Kudu da Tsakiyar Asiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 3

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 3 don bayanai kan Abdul Wali, wanda aka sani kuma da Omar Khalid Khorasani. Wali ne jagoran ƙungiyar Jamaat ul-Ahrar (JuA), ɓangaren ‘yan gwagwarmaya mai alaƙa da Taliban a Pakistan (Tehrik-e Taliban Pakistan – TTP), wadda Amurka ta ayyana a matayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje. A ƙarƙashin jagorancin Wali, JuA ta kasance ɗaga cikin ƙungiyoyi ƙawayen TPP da suka fi gudanar da ayyuka yankin Punjab na Pakistan kuma ta ɗauki alhakin kai hare-hare masu yawa a faɗin Pakistan.

Rahotanni sun ce Wali na aiki ne daga yankunan Nangarhar da Kunar na Afghansitan. An haifi Wali Mohmand Agency da ke Pakistan. Tsohon ɗan jarida ne kuma mawaƙi, wanda ya yi karatu a makarantu da yawa a birnin Karachi na Pakistan.

Skip to content